• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR ‘YAN SANDA TA CAFKE AJODO LAWYENCE DA YA JAGORANCI KUTSE GIDAN MARY ODILI

ByNasiru Adamu El-hikaya

Nov 13, 2021

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta baiyana cafke mutum 14 da a ke tuhuma da kutsawa gidan Jostis Mary Odili da ke anguwar Maitams Abujs.
Cikin wadanda a ke cafken har da jami’in ‘yan sanda na bogi CSP Ajodo Lawrence wanda ya jagoranci kutsen don kwashe wasu tulin kudi da a ka ce su na jibge a gidan.
A sanarwa daga kakakin rundunar Frank Mba, duk wadanda a ka cafken ba su da wata alaka da wata hukumar gwamnati.
A yanzu haka a na neman mutum 7 don gurfanar da su gaban kotu.
Jostis Mary Odili dai ita ce ta biyu mafi girman mukami a kotun kolin Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *