• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR ‘YAN SANDA TA BUKACI BA DA LABARIN DAMFARAR YANAR GIZO A MANHAJAR TA TA AIKIN KASA DA KASA

ByNoblen

Sep 15, 2022

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bukaci jama’a su taimakawa manhajar ta, ta yanar gizo ta tara bayanan damfarar yanar gizo da cin zarafi da hakan ya hada da aikin ‘yan sanda na kasa da kasa waton INTAFOL.

Babban sufeton ‘yan sandan Usman Baba Alkali ya mika bukatar da ya ce hakan zai taimakawa rundunar wajen musayar samun bayanai da sauran kasashe da ke cikin rundunar ‘yan sandan kasa da kasa su 195.

Kazalika manhajar za ta taimaki masu ziyartar ta da bayanai sabbin hanyoyin kare kai daga ‘yan damfarar yanar gizo da su ka addabi jama’a.

Babban sufeto Alkali ya ba da umurnin kammala aikin ginin sabon ofishi da ked aura da helkawatar ‘yan sandan (Gidan Luois Edet) a Abuja inda jami’an bayanan sirrin ‘yan sandan za su yi aiki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “RUNDUNAR ‘YAN SANDA TA BUKACI BA DA LABARIN DAMFARAR YANAR GIZO A MANHAJAR TA TA AIKIN KASA DA KASA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.