• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR ‘YAN SANDA A ZAMFARA TA CETO WADANDA A KA SACE 24

ByNasiru Adamu El-hikaya

Nov 25, 2021

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta baiyana ceto mutum 24 da ‘yan bindiga su ka sace da su ka shafe kwana 60 a hannun miyagun irin.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Ayuba Elkana ya ce an ceto mutanen da su ka hada da dalibai a yankin karamar hukumar Shinkafi da Tsafe.
An sace daliban ne ma lokacin da su ke rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandare.
Rundunar ta ce an sako mutanen ba tare da wani sharadi ba.
Ba wani sabon abu ba ne sace mutane don karbar kudin fansa a jihar Zamfars da kewaye.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.