• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR ‘YAN SANDA A ZAMFARA TA BA DA TABBACIN KARE MASU YI WA KASA HIDIMA BAYAN SACE WASU DAGA CIKIN SU

ByNoblen

Oct 24, 2021

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta karfafawa matasa masu yi wa kasa hidima a jihar guiwa cewa za ta tabbatar tsaron lafiyar su.

Wannan tabbaci ya zo ne bayan sace wasu daga matasan yayin da su ke kan hanyar tafiya sansanin horar da su makamar aikin hidimar a Tsafe.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ayuba Elkana ya ziyarci sansanin horarwar inda ya tabbatarwa matasan matakan da a ke dauka don kare su daga barayin mutane.

Yanzu dai rundunar ta ce ta tura jami’ai don ceto matasan da a ka sace da sauran wadanda akasin ya rutsa da su.

In za a tuna dai an dawo da sadarwar wayar salula a babban birnin jihar Gusau da hakan ya farfado da hada-hada da walwalar al’umma.

Jihar Zamfara na daga mafi tsanantar fama da barayin daji da kan sace da karbar kudin fansa.

Jami’an tsaro sun kaddamar da yaki da miyagun irin da su ka addabi akasarin yankin arewa maso yammacin Najeriya da kuma jihar Neja a arewa ta tsakiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “RUNDUNAR ‘YAN SANDA A ZAMFARA TA BA DA TABBACIN KARE MASU YI WA KASA HIDIMA BAYAN SACE WASU DAGA CIKIN SU”
  1. Admiring the hard work you put into your site and in depth information you offer.
    It’s great to come across a blog every once in a while that isn’t the same outdated rehashed material.
    Excellent read! I’ve saved your site and I’m adding
    your RSS feeds to my Google account.

Leave a Reply

Your email address will not be published.