Rundunar taron dangin yaki da ‘yam tawayen houthi a Yaman da Saudiyya ke jagoranta ta ragargaza wani jirgin ruwa shake da nakiyoyi na houthi kirar Iran a Bahar Maliya.
Houthi dai ta shirya kai hari ne daga tashar jiragen ruwa ta Yaman wato Hodeida.
Saudiyya da sauran kasashe na nuna damuwa yanda houthi ke barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a Bahar Maliya ta kai hare-hare da taimakon Iran.
Daular Larabawa da Bahrain sun yi tir da matakan take dokokin duniya da houthi ke yi ta kai hare-hare da amfani da jirage marar sa matuka kirar Iran.
Daular Larabawa ta zargi houthi da cewa ta na barazana ga salama a daukin yankin gabar ta tsakiya.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀