• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR YAKI DA HOUTHI TA KAKKABO MAKAMIN DA HOUTHI TA CILLA KUDANCIN SAUDIYYA

ByNoblen

Apr 7, 2021

Rundunar taron dangi da Saudiyya ke jagoranta ta yaki da ‘yan tawayen houthi a Yaman ta kakkabo makamin da ‘yan tawayen su ka cilla kan yankin kudancin Saudiyya.

Jirgin dai marar matuki ne, houthi ta cilla shi ne kan garin Khamis Mushayt.

A kan ga makaman da houthi kan cilla kan Saudiyya kirar Iran ne.

Rundunar ta ce houthi na saba dokokin duniya wajen kai hari kan yankunan fararen hula.

Har yanzu houthi ke rike da babban birnin Yaman wato Sanaa inda zababbiyar gwamnati ta Abed Rabbo ke aiki daga garin Aden na kudanci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *