• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR SOJAN NAJERIYA TA SAUYA WAJAJEN AIKI GA MANYAN JAMI’AN TA

ByYusuf Yau

Jul 5, 2021 ,

Rundunar sojan Najeriya ta yi sauye-sauye a mukaman rundunar na sassa daban-daban da ya biyo bayan garambawul.

Sabon babban hafsan sojan kasa Manjo Janar Farouk Yahaya ne ya amince da sauye-sauyen don sabon zubi ga aiyukan rundunar da ya zama bisa al’ada su sauya tun da an samu rasuwar tsohon babban hafsa Kanar Attahiru Ibrahim a hatsarin jirgin sama.

Cikin wadanda su ka baiyana a mukaman da I.M. Yusuf ya zama babban kwamandan makarantar horar da manyan hafsoshin soja ta Kaduna NDA.

Shi kuma Manjo Janar T.A.Gagariga ya sama kwamandan rundunar sojojin tankokin yaki.

Hakanan shi kuma V.O. Ezugwu ya zama kwamandan sojoji masu artabu a kasaa fagen daga.

Ba wani sabon abu ba ne wadannan sauye-sauyen.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *