• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR SOJAN NAJERIYA TA BUKACI A YI WATSI DA WANI BIDIYO DA TA CE FARAFAGANDA NE

Rundunar sojan Najeriya ta bukaci jama’a su yi watsi da wani faifan bidiyo da ta ce na farafaganda ne don illa ga martabar soja a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Bidiyon na nuna wasu masu shigen sojoji na wargaza wata gona.

Kakakin sojojin Onyeama Nwachukwu ya ce masu yada bidiyon na son nuna sojan Najeriya ba sa kaunar jama’a.

A binciken da rundunar ta gudanar ya nuna tun farko wani shafin ‘yan awaren Biafra ya fara sanya faifan.

Nwachukwu ya ce masu faifan ba su fadi ka a wace jiha ko waje lamarin ya auku ba.

Kakakin ya ce tabbas soja za su cigaba da aiki ba tare da biyewa karkatar da hankali na farafaganda ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *