• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR SOJA TA YI ALWASHIN MURKUSHE ‘YAN BINDIGA A KEBBI

Rundunar sojan Najeriya ta yi alwashin yin dirar mikiya kan dukkan ‘yan bindigar jihar Kebbi bayan aranmgamar da ta yi sanadiyyar mutuwar sojoji 18 inda biyu su ka bace.
Akasin ya auku ne a karamar hukuamr Danko-Wasagu lokacin da mataimakin gwamnan jihar Sma’ila Yombe da kwamandan sojoji na jihar ke ziyara a yankin.
Rahoto ya nuna hatta mataimakin gwamnan ya tsallake rijiya da baya ne.
An ga wani faifan bidiyo da ke nuna matan sojojin da a ka kashe sun yi fushi su na masu zanga-zanga a gidan babban jam’in sojin jihar da baiyana cewa sam ba zsu yard aba.
Tun sace daliban makarantar sakandaren Yawuri a ka kara zafafa fafatawa da ‘yan bindigar amma haka ba ta tadda ruwa ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “RUNDUNAR SOJA TA YI ALWASHIN MURKUSHE ‘YAN BINDIGA A KEBBI”
  1. Oh my goodness! Amazing article dude! Many thanks, However
    I am encountering difficulties with your RSS. I don’t know the reason why I am unable to subscribe to it.
    Is there anybody else getting similar RSS issues? Anybody who knows
    the answer will you kindly respond? Thanx!!

Leave a Reply

Your email address will not be published.