• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR LARABAWA TA RAGARGAZA KANANAN JIRAGEN RUWA 4 NA HOUTHI

Rundunar larabawa ta yunkurin dawo da zababbiyar gwamnatin Yaman ta kai harin da ya ragargaza kananan jiragen ruwan ‘yan tawayen houthi 4.
An ragargaza jiragen ne a tashar teku ta Saleef da kuma Hodeida.
‘Yan tawayen na houthi da Iran ke marawa baya su na kan hada jiragen da za su kai hari kan jiragen ruwa, yayin da a ka kawar da illar da su ke shirin haifarwa.
Houthi na rike da babban birnin Yaman San’a’a tun 2014 da hana zababbiyar gwamnatin Yaman ta Abed Rabbo Mansour Hadi aiki, da hakan ya tilastawa gwamnatin aiki daga birnin Aden na kudancin kasar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “RUNDUNAR LARABAWA TA RAGARGAZA KANANAN JIRAGEN RUWA 4 NA HOUTHI”
  1. Hi there would you mind sharing which blog platform you’re working with? I’m planning to start my own blog in the near future but I’m having a hard time deciding between BlogEngine/Wordpress/B2evolution and Drupal. The reason I ask is because your design seems different then most blogs and I’m looking for something completely unique. P.S My apologies for getting off-topic but I had to ask!

Leave a Reply

Your email address will not be published.