• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR LARABAWA TA NUNA SHAIDAR HANNUN HEZBOLLAH A YAKIN BASASAR YAMAN

ByNoblen

Dec 27, 2021 ,

Rundunar larabawa da Saudiyya ke jagoranta ta nuna shaidar hannun kungiyar shia ta Hezbollah a fitinar da ta hana Yaman zaman lafiya da kuma yanda ‘yan tawayen houthi su ma ‘yan shia da Iran ke marawa baya ke kai hare-hare cikin Saudiyya.
A taron manema labaru a Riyadh, kakakin rundunar Burgediya Janar Turki Almaliki ya nuna faifan bidiyon ‘yan Hezbollah na koyawa ‘yan houthi yanda a ke harba jirgi marar matuki da a kan yi amfani da shi musamman don kai hare-hare kudancin Saudiyya.
Hakanan Hezbollah na amfani da filin jirgin saman San’a’a babban birnin Yaman don harar da ‘yan houthin kan sarrafa makamai.
Almaliki ya ce jakadan Iran a San’a’a Hassan Irloo wanda yam utu makwan jiya a sanadiyyar korona, shi ke ba da umurnin yakin da ‘yan houthi ke yi a kan yankin Marib mai arzikin iskar gas da ke hannun gwamnatin kasar ta Abed Rabbo.
Daga janairun 2018, Almaliki ya ce houthi ta harba makamai masu linzami 430 da jirge marar sa matuka 851 zuwa Saudiyya, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Saudiyya 59.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *