• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR LARABAWA TA KAI FARMAKI KAN TUNGAR ‘YAN HOUTHI A SAN’A’A

ByNoblen

Dec 26, 2021 ,

Rundunar larabawa da Saudiyya ke jagoranta ta kai farmakin jiragen yaki kan sassan ‘yan tawayen houthi mabiya shia a babban birnin Yaman wato San’a’a.
Rundunar ta buakci fararen hula kar su taru ko tinkari sassan da a ka kai harin, inda ‘yan tawayen na houthi ke tara makamai.
Gidan talabijin na Al-Ekbariyya ya baiyana cewa rundunar ta kai harin ne biyo bayan samun wata barazana daga ‘yan tawayen.
Tun farko rundunar ta ce ta kai hare-hare 40 kan ‘yan houthi a yankin Marib inda ‘yan tawayen 223 su ka hallaka da lalata motocin yaki 17.
Hakanan rundunar a lahadin nan za ta yi bayani da nuna shaidun shigowar kungiyar Hezbollah ta ‘yan shia ta Lebanon a yakin basasar Yaman da neman kai hare-hare cikin Saudiyya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *