• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR LARABAWA TA FARA KAI HARE-HARE KAN SASSAN HOUTHI A SAN’A’A

Rundunar hadin guiwar larabawa da ke yaki da ‘yan tawayen houthi a Yaman ta kaddamar da sabbin hare-hare kan sassan ‘yan tawayen da Iran ke marawa baya.
Hare-haren za su dira ne a wajajen da ‘yan tawayen ke amfani da su don lamuran ‘yan bindiga a babban birnin Yaman wato San’a’a.
Rundunar ta ce ta yi hakan ne don kare farar huka da sojojin da ke fafatawa don karfafa zababbiyar gwamnatin Yaman ta shugaba Abed Rabbo da ke aiki daga birnin Aden na kudanci.
Hakanan rundunar ta kai sawun hari 14 kan ‘yan tawayen a yankin Marib da Al-bayda a sa’a 24 da su ka wuce inda hakan ya yi sanadiyyar hallaka fiye da ‘yan tawayen 50 da motocin yaki 9.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.