• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR LARABAWA TA DAKILE HARIN HOUTHI KAN JAZAN

ByNoblen

Apr 9, 2021

Rundunar taron dangi ta larabawa da Saudiyya ke jagoranta ta dakile harin makami mai linzami da ‘yan tawayen houthi su ka hsrba kan kudancin Saudiyya.

Houthi dai da Iran ke marawa baya ta auna harin kan garin Jazan da ke kudancin kasar ta Saudiyya.

Tun farko dai rundunar ta dakile hari biyu na houthi kan garin Khamis Mushayt da kuma yankin kudancin.

Rundunar da ke aikin karfafa zababbiyar gwamnatin Yaman ta Abed Rabbo, ta ce za ta dau duk matakan da ba su sabawa dokokin duniya ba wajen kare rayukan fararen hula.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *