Rundunar hadin kan larabawa da Saudiyya ke jagoranta ta baiyana cewa ta kai hari a yankin Marib da Albayda inda fiye da ‘yan tawayen houthi 100 su ka hallaka.
Rundunar ta ce a harin na jiragen yaki cikin sa’a 24 da su ka wuce an lalata motocin yakin ‘yan tawayen 19 da kuma lalata kayan aikin yakin samaniya.
Hakanan rundunar ta kai hari a bakin tekun yammacin kasar don ba wa dakarun ruwa karfin guiwar gudanar da yaki da ‘yan tawayen da Iran ke marawa baya.
Wani labari daga rundunar ya ce ‘yan houthi sun yi yunkurin harba makamai masu linzami daga babban birnin kasar Sanaa wadanda su ka fada wani sashe na Yaman.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Wonderful article! We are linking to this particularly great post on our website. Keep up the great writing.