• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR LARABAWA TA AIYANA GAGARUMIN FARMAKI DON GAMAWA DA ‘YAN TAWAYEN HOUTHI

Rundunar hadin guiwar larabawa da Saudiyya ke jagoranta ta kaddamar da aniyar gagarumin farmaki ko ta wane bangare don gamawa da ‘yan tawayen houthi ‘yan shia da Iran ke marawa baya.
Wannan ya biyo bayan nasara kan ‘yan tawayen a Shabwa.
Kakakin rundunar Burgediya Janar Turki Almaliki ya baiyana muradin a taron manema labaru a Shabwa da halartar gwamnan jihar Awadh Muhammad Al-Awlaki.
Almaliki ya ce nasarar ‘yantar da Shabwa bayan kakkabe ‘yan tawayen daga gundumar Ain, ya zama hanyar hada kan ‘yan Yaman wajen kawo karshen tawaye a kasar su.
Houthi dai tun 2014 ta tada fitina da mamaye babban birnin Yaman wato San’a’a inda hakan ya tilasatwa gwamnatin kasar kafa helkwatar wucin gadi a garin Aden na kudanci kuma shugaban kasar Abed Rabbo na zamane a birnin Riyadh.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “RUNDUNAR LARABAWA TA AIYANA GAGARUMIN FARMAKI DON GAMAWA DA ‘YAN TAWAYEN HOUTHI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *