• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR HADIN GUIWAR LARABAWA TA KAI HARI KAN SASSAN HADA MAKAMAN ‘YAN TAWAYEN HOUTHI A FILIN JIRGIN SAN’A’A

ByNoblen

Dec 21, 2021 , ,

Rundunar hadin guiwa ta larabawa da Saudiyya ke jagoranta ta kai hari sassan babban filin jirgin saman San’a’a da ‘yan tawayen houthi na Yaman ke amfani da su wajen hada makamai.
‘Yan tawayen dai sun shiga amfani da filin jirgin wajen harhada makamai ciki da harba jirgi marar matuki musamman kan kudancin Saudiyya.
Kakakin rundunar Burgediya Janar Turki Almaliki ya ce an sanar da ofishin jinkai na majalisar dinkin duniya a filin jirgin sa’a daya kafin kai farmakin.
Harin ya shafi sassa 6 da houthi ke amfani da su wajen kai hare-hare da jirage marar sa matuka.
Almaliki ya ce rundunar ta yi iya bakin kokari wajen kaucewa taba fararen hula a harin.
Houthi da ke da goyon bayan Iran na cigaba da babakere a babban birnin kasar San’a’a ta hanyar hana zababbiyar gwamnatin Abed Rabbo zama a birnin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *