• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUGUGIN YAKI YA SA SOJA YA HARBA ALBARUSHI YA KASHE JAMI’IN KWASTAM A SEME

Da alamu rugugin yaki ya tabs kwakwalwar wani soja wanda ya harba bindiga har harsasi ya kashe jami’in kwastam mai suna Walter a kan iyakar Seme da ke Lagos.

Sojan dai mai suna Mahmud Sulaiman da a ka kawo Lagos daga yaki a Borno, ya rika cika bindigar sa ne da albarusai ya na rike kunama kamar zai bude wuta.

Wannan dalilin ya sanya ba da umurnin amshe bindigar amma sam Sulaiman ya shiga gardama har ya bude wuta harsashi ya samu jami’in na kwastam.

Ganin ya yi kisan gilla sai Sulaiman ya juya kunamar kan sa ya budewa kan sa wuta a nan take ya mutu.

Lamarin ya ba da takaici da tausayi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
47 thoughts on “RUGUGIN YAKI YA SA SOJA YA HARBA ALBARUSHI YA KASHE JAMI’IN KWASTAM A SEME”

Leave a Reply

Your email address will not be published.