• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ROTIMI AMAECHI YA AIYANA TSAYAWA TAKARAR SHUGABANCIN NAJERIYA

A karshe ministan sufuri Rotimi Amaechi ya aiyana niyyar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2023.
An kwan biyu a na raderadin Amaechi wanda tsohon gwamnan jihar Ribas ne na son yin takarar.
Amaechi wanda ya ba da gagarumar gudunmawa a zaben da shugaba Buhari ya lashe a 2015, ya zama daya daga manyan ministoci a gwamnatin ta APC.
Ganin Sarkin Daura a jihar Katsina inda nan ne mazabar shugaba Buhari ya ba shi sarautar gargajiya, ya sa kara tunanin cewa hakan alama ce ta cewa ba mamaki Amaechi na samun goyon bayan wasu ‘yan arewa.
Tuni Bola Tinubu, Rochas Okorocha da mataimakin shugaba Buhari wato Yemi Osinbajo su ka aiyana neman tikitin APC.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.