Rokokin houthi sun dira a yankin Taiz mai tashar jirgin ruwa ta gabashin kasar Yaman duk da yunkurin sulhu da majalisar dinkin duniya ke yi na kawo karshen fitina a kasar.
Jami’in sojan Yaman Abdulbasit Al-Baher ya ce rokokin Yaman sun fada kan yankin na Taiz inda a ka auna yankunan farar hula.
Houthi na daukar matakan da su ke hannun riga da kawo salamar da majalisar dinkin duniya ke jagoranta karkashin jakadan ta Hans Grungberg.
Shugaban gwamnatin Yaman a birnin Aden na kudanci Rashad Al-Alimi ya na fatar samun daidato da zai tabbatar da daina bude wuta tsakanin gwamnatin da ‘yan tawayen da Iran ke marawa baya.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀