• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ROKOKI 3 SUN DIRA A CIBIYAR SOJAN IRAKI DA KE DAF DA BIRNIN BAGADAZA

Wasu rokoki uku sun yi dirar mikiya kan cibiyar sojan saman Iraki dake daf da birnin Bagadaza inda ‘yan kwangilar Amurka ke zama.

A cibiyar a ke adane da jirgin yaki kirar F-16 da Iraki ta sayo daga Amurka da kuma ‘yan kwangilar ke kula da su.

Helkwatar tsaron Amurka Pentagon ta ce ba wanda ya samu rauni a sanadiyyar harin.

Kimanin rokoki 30 ne a ka harba kan muradun Amurka a Iraki tun hawan sabon shugaban Amurka Joe Biden.

Amurka kan aza laifin irin wannam hari kan kungiyoyin aware na Iraki da Iran ke marawa baya.

In za a tuna Amurka a zamanin mulkin tsohon shugaba Donald Trump ta kai farmaki a filin saukar jiragen sama na Bagadaza inda ta hallaka babban kwamandan kasar Iran Kassim Soulaimani da hakan ya jawo bakin cikin ainun daga hukumomin Iran mabiya darikar shia.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *