• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RIJIYAR MALABU: ADOKE YA KALA MANA ABUN DA BA MU YI BA-KUNGIYAR YAKI DA CIN HANCI TA HEDA

Wata kungiyar yaki da cin hanci da rashawa HEDA a takaice ta dau matakin kai karar tsohon ministan shari’ar Najeriya Bello Adoke a gaban babbar kotun birnin Abuja don zargin ya yi ma ta kage.

HEDA ta ce Bello Adoke ya fitar da sanarwar cewa ta kirkiro shaidar zur a shaidar da ta bayar a gaban kotu a birnin Milan na Italiya kan shahararriyar badakalar nan ta sayar da rijiyar man fetur ta Malabu.

Kungiyar HEDA karkashin lauyan ta Kunle Adegoke na bukatar kotu ta tilasta Adoke ya janye sanarwar ya kuma biya ta diyyar Naira miliyan 100.

Har yanzu tsohon ministan na fuskantar shari’a kan badakalar sayar da rijiyar ta man fetur ta Malabu mai lamba 245.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *