• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RIGAKAFIN KORONA GA RUKUNI NA FARKO A NAJERIYA YA KAI KASHI 55%

Rigakafin da a ke gudanarwa rukuni na farko na korona a Najeriya ya cimma yi wa mutum miliyan 1,114,408.

Alkaluma sun nuna an yi wa kashi 55% rigakafin da nasarar karin kashi kimanin kashi 2% a wajen mako daya da ya gabata.

Duk da allurar zagaye na farko ne, inda wadanda su ka samu rigakafin ke rike da ranar da za a yi mu su allura ta biyu.

An raba kason rigakafin na korona daga tsarin tallafin COVAX mai tallafawa kasashe masu tasowa ga jihohin Najeriya.

Akalla akwai rahotannin korafin zazzabi ga wasu da a ka yi wa allurar ta AstraZeneca da hadin guiwar jami’ar Oxford.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.