• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RIGAKAFI-KARIYAR FUSKA TA RAGU KWARAI HAR A BABBAN BIRNIN NAJERIYA

Da alamu yin rigakafin cutar korona da manyan ‘yan bokon Najeriya su ka yi har zagaye biyu ya rage yanda a ke sanya kariyar fuska da kan badda kamannin mutane.

Dama ba a faye sanya kariyar ba hatta lokacin da cutar ke kaifi bara a jihohi da dama na Najeriya musamman yankunan karkara.

Yanzu haka a Abuja mutane kan iya shiga manyan shaguna da kasuwanni ba tare da an tilasta mu su sanya kariyar ba duk da akwai takarda manne da ke nuna ba shiga sai da kariyar fuska.

Matasa a kan tituna na shafe tsawon lokaci su na tallar kariyar amma ba sa samun kasuwa.

Wani dalilin kuma na rashin sanya kariyar shi ne ga wadanda kariyar kan hana su shakar wadatacciyar iska har ka ga su na neman galabaita.

Akwai kuma mutanen da su ka ki jinin kariyar ainun da tsanar duk wanda su ka gani ya sanya kariyar musamman mai shigen zunguru ko na tsummar zani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.