• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

REDIYON HUMAN RIGHTS YA DAKATAR DA GIDAUNIYAR TARA KUDI DON ASUU SU DAWO AIKI

Gidan rediyon HUMAN RIGHTS da ke Abuja ya dakatar da gidauniyar tara kudi don mika su ga kungiyar malaman jami’a na Najeriya ASUU don su dawo aiki.

ASUU dai a halin yanzu na cikin yajin aikin tilasta gwamnati ta biya bukatun alawus, gyara jami’o’I da sauran su da hakan ya kai biliyoyin Naira.

Tun farko shugaban gidan rediyon Ahmed Isah ya bude ma’ajiyun banki biyu don tara kudin da za a mikawa ASUU don malaman su dawo aiki, ‘ya’yan talakawa su koma makaranta.

Isah ya ce tuni an samu gudunmawar miliyoyin Naira ciki har da Naira miliyan 50 da gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ya bayar.

Shugaban kungiyar malaman Farfesa Emmanuel Osodeke ya bukaci cire sunan ASUU a sunan asusun da a ka bude, ya na mai nuna fargabar amincewa da hakan zai kawo zargin ASUU ta karbi kudi daga gidan rediyon.

Osodeke ya ce manufar gidan rediyon mai kyau ce amma su dai a cire sunan su don kudin da su k enema daga hannun gwamnati ba su a ke ba wa kai tsaye ba, jami’o’I a ke mikawa.

Nan take Isah ya ce ya dakatar aikin gidauniyar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.