• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN ZUWA HAJJIN BANA-NAHCON TA TARA JAMI’AN LABARUN ALHAZAI A ABUJA

Biyo bayan dakatar da damar zuwa hajji shekaru biyu a jere da Saudiyya ta yi don kalubalen korona bairos,  hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta tara dukkan jami’an labarun hukumomin alhazai na jihohi don bitar halin da a ke ciki.

NAHCON ta ce ya zama wajibi a samu bayanai na bai daya ga maniyyata don ba su kwarin guiwar cewa da yardar Allah za su cimma burin sauke faralin.

Shugaban hukumar Zikrullah Kunle Hassan ya ce duk da rashin zuwa hajjin, hukumar na cigaba da tsare-tsare kan yanda za a tunkari zuwa hajjin da zarar an bude dama don amfanin dubban maniyyata daga Najeriya.

Kunle Hassan wanda a shekarar da ya hau mukamin jagorancin hukumar duniya ta fada kalubalen korona, ya ce wajibi ne hukumar ta rika samar da bayanai ga maniyata don zama cikin shirin gujewa fafa gora ranar tafiya.

Jami’ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara ta yi bayani filla-filla kan kalubalen da matakan da hukumar ke dauka.

Mahalarta taron sun baiyana irin tambayoyin da su ke samu daga maniyata kan aikin hajjin da ya ke cikin runkunan musulunci biyar.

A gefe guda hukumar ta na kara inganta shirin adanar kudi don samun gudanar da aikin hajji ta hanyar ajiyar kudi na tsawon lokacin da maniyyaci zai iya tara kudin kujera.

Kamar yanda shugaban sashen Dr.Aliyu Tanko ya fada, tsarin tamkar wanda a ke yi ne a Malaysia inda mai niyya zai yi ta tara kudi har ya samu damar akalla ya je hajji a rayuwar sa sau daya.

NAHCON da a ka kafa a 2006 daga sashe a ma’aikatar waje;   kan zama mai shiga yarjejeniya a madadin jihohi kan aikin hajji da Saudiyya 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *