• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN TSARO NA TA’AZZARA A JIHAR KEBBI DON SACE DALIBAI A YAWURI

ByYusuf Yau

Jun 18, 2021 , , ,

Yanzu dai murnar zaman lafiya a jihar Kebbi ta zama tarihi don yanda a ka sace dalibai a sakandaren yankin Yawuri.

‘Yan bindigar sun shigo Yawuri daga jihar Neja kan babura inda su ka bude wuta kan masu gadin makarantar kafin samun damar kwashe dalibai da ma wasu malamai.

Maharan sun kashe dan sanda daya da tafiya da daliban da malamai uku.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kebbi ta ba da tabbacin tura jami’ai da ke bin sawun barayin don kokarin kwato daliban.

Wannan akasin na neman zama ruwan dare da ke hana iyaye, malamai da dalibai barci don yiwuwar kawo hari a koyaushe daga miyagun iri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.