• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN SAMUN SAUYIN KUJERUN HAJJI DUBU 60 BANA -ZAISA KASASHE KA IYA TASHI DA ALHAZAI DUBU DAYA

Bisa bayanin kason kujeru dubu 60 da Saudiyya ta ware don hajin bana, alamu na nuna matukar ba a samu sauyi ba, to kasahe ka iya tashi da alhazai dubu daya a hajjin na bana wanda ke dada karatowa.

Abun dubawa a cikin kujerun dubu 60, an ware dubu 45 ga dukkan kasashen duniya inda dubu 15 za su fito daga cikin Saudiyya.

A baya dai gabanin annobar korona, Najeriya ita kadai na samun kason kujeru dubu 95 kuma a yi rububin neman su, amma a aikin hajjin 2019 don kuncin tattalin arziki alhazan ba su fi kimani dubu 45 din ba da yanzu a ka warewa dukkan duniya.

A gaskiya akwai juyayi ainun na yanda lamura su ka sauya game da aikin hajji da fiye da mutum miliyan 2 ke zuwa a baya gabanin wannan annobar.

A bara mutum dubu daya ne kacal su ka gudanar da aikin hajji sai kuma ba mamaki aljannu da ba a iya gani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.