• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN SAMUN KWANGILA YA SANYA MBAKA CACCAKAR SHUGABA BUHARI-FADAR ASO ROCK

ByYusuf Yau

May 1, 2021

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce jagoran nan na sashen mabiya darikar katolika a Najeriya Reverend Ejike Mbaka ya nemi a ba shi kwangila ne bai samu ba shi ya sa ya shiga caccakar shugaba Buhari.

In za a tuna Mbaka ya goyi bayan shugaba Buhari a zaben 2015 da kuma 2019 amma kwanan nan ya bukaci shugaban ya yi murabus da nuna ya gaza.

A martani daga mai taimakawa shugaban kan labaru Garba Shehu ya ce Mbaka ya nemi ganawa da shugaban sai ya shigo da wasu ‘yan kwangila uku su ka yi zama da shugaba Buhari inda a nan ya nemi a ba shi kwangila don ya zama diyyar goyon bayan da ya bayar.

Shugaba Buhari ya dau matakin a bi ka’idar ba da kwangila don tabbatar da gaskiya da amana maimakon amfani da karfin gwamnati don ba wa Mbaka abun da ya nema.

Shehu ya ce fadar ta ga bai dace ba ne ta buda sirrin irin abubauwan da Mbaka ya nrma don kar mabiyan sa su juya ma sa baya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *