• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN NIN-SAMA DA LAYUKAN WAYA MILIYAN 72 A KA RUFE A NAJERIYA

ByYusuf Yau

Apr 12, 2022 , ,

Hukumar kula da kamfanonin sadarwar salula NCC ta Najeriya ta ce layukan wayar da zuwa yanzu ba a hada su da lambobin shaidar dan kasa ba wato NIN an rufe su.
An fara aikin hada kayukan da NIN tun 2020 inda a ka rika dagewa rufe layukan har sau 10 don ba da dama ga ma’abita salula su kammala rejistar.
Labarin ya nuna cewa zuwa yanzu sana da layuka miliyan 72 a ka rufe don rashin hada su da NIN.
Gwamnatin Najeriya na nuna matakin na da nasaba ne da inganta lamuran tsaro ta hanyar gano ‘yan ta’adda da ke amfani da layukan salula.
Masu satar mutane kan yi amfani da layukan salula wajen ciniki don karbar kudin fansa hakanan miyagun kan yi sadarwa a tsakanin su wajen shirya miyagun aiyuka.
Akalla dai wasu ‘yan Najeriya sun ba da labarin daina aikin wasu daga layukan su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “RASHIN NIN-SAMA DA LAYUKAN WAYA MILIYAN 72 A KA RUFE A NAJERIYA”
  1. Hello! And keep going, "RASHIN NIN-SAMA DA LAYUKAN WAYA MILIYAN 72 A KA RUFE A NAJERIYA" very interesting topic !

Leave a Reply

Your email address will not be published.