• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN MUTUNTA DOKOKIN HANYA NA TA’AZZARA A ABUJA

ByYusuf Yau

Jun 25, 2021 , ,

Kalubalen rashin bin dokar hawa titi na kara ta’azzara a Abuja babban birnin Najeriya inda wasu matuka mota kan yi biris da umurnin danja.

Matukar mutum ya na yawo a birnin sai ya ga inda a ka yi wani hatsari mai ban mamaki to ba munimmin dalilin yin hatsarin fiye da rashin bin dokokin hanya.

Za ka ga tamkar kowa ya na ta kan sa ne ba tare da taimakawa ko saurarawa sauran masu amfani da titi ba.

Ba ma titi kadai ba, direba zai hango inda ruwa ya mamale titi ga mutane na tafiya da kafa a gefen titin amma sai ya sheko da gudu ya ratsa ruwan ya watsawa mutane ba tare da ya rage wuta ko ma ya damu da abun da ya aikata ba.

Hakan na nuna wasu mutanen su na rayuwa ne bisa miracun kashin kan su ba tare da sanin akwai wani mai hakki ba.

Ga dokar hanya kuma, matukar ba an sanya irin kamarorin nan na kasashen da ke bin doka ba, a na jiggawa masu taka doka makudan kudin tara su na biya, ba za a rabu da wannan taka doka na rashin sanin ya kamata ba.

Kazalika ya dace a rika kwace motocin wadanda su ka aikata laifi fiye ma da janye lasisin su, don direba kan iya tuka mota a Najeriya ko ba lasin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “RASHIN MUTUNTA DOKOKIN HANYA NA TA’AZZARA A ABUJA”
  1. I just couldn’t depart your website prior to suggesting that I actually loved the standard info a person supply to your visitors?
    Is going to be again steadily in order to investigate cross-check new posts

  2. I’m impressed, I have to admit. Seldom do I come across
    a blog that’s both equally educative and amusing, and without a doubt, you have hit the
    nail on the head. The issue is something which too few men and women are speaking intelligently
    about. I’m very happy that I stumbled across this in my search for something regarding this.

Leave a Reply

Your email address will not be published.