• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN KYEN YANAYIN SAMANIYA YA HANA SHUGABA BUHARI ZIYARTAR JIHAR ZAMFARA

Kalubalen rashin kyawun yanayi ya dakatar da shugaba Buhari daga ziyartar jihar Zamfara daga Sokoto don jajantawa al’ummar jihar bisa yawan hare-hare ‘yan bindiga da kan yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi.
Shugaban wanda ya shiga Sokoto da duba kamfanin siminti na BUA, ya so ya zarce Zamfara da jirgi mai saukar angulu amma rashin kyawun yanayi ya sa ya janye.
Bayan dawowar sa Abuja, shugaban ya yi jawabi a faifai na sakon baiyana uzurin da ya sa bai shiga Zamfara ba, ya na mai cewa nan gaba in ya samu lokaci zai kawo ziyarar.
Shugaban ya godewa gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun da yanda ya shirya tarba amma hakan bai tafi yanda a ke so ba don yanayi.
An sha gorantawa shugaba Buhari kan rashin ziyartar Sokoto da Zamfara da ‘yan bindiga kan ci Karen su ba babbaka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
49 thoughts on “RASHIN KYEN YANAYIN SAMANIYA YA HANA SHUGABA BUHARI ZIYARTAR JIHAR ZAMFARA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.