Kafafen yanar gizo sun cika da korafin rashin halartar akasarin manyan jami’an gwamnatin Najeriya wajen jana’izar babban hafsan rundunar sojan kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da ‘yan tawagar sa da su ka mutu a hatsarin jirgin sama.
Daga sallah a babban masallacin Abuja zuwa makabartar sojoji ta hanyar filin saukar jiragen sama, ba a ga akasarin manyan jami’an gwamnatin Najeriya ba ciki kuwa har da madugu uban tafiya shugaba Muhammadu Buhari.
Duk da gwamnatin ta nuna kaduwa ainun ga rashin, ba a ga wata tawaga mai karfi daga fadar Aso Rock wajen jana’izar ba.
Duk da dai ba a ba da dalilan matakan kaucewa cutar korona ne su ka jawo rashin baiyanar ba, rashin wata tawaga mai karfi ta bar masu baiyana ra’ayi da cewa gwamnatin ba ta samu shawara mai kyau kan lamarin ba.