• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHIN FITOWAR JAMA’A YA RAGE ARMASHIN ZABEN JIHAR ANAMBRA

ByYusuf Yau

Nov 9, 2021

Rashin fitowar masu kada kuri’a yanda ya dace ya rage armashin zaben gwamnan jihar Anambra da dan takarar jam’iyyar APGA Charles Soludo ya yi wa sauran ‘yan takara fintinkau.

Tuni dai hukumar zaben ta aiyana zaben a matsayin wanda ba a kammala ba.

Kwamishina a hukumar zaben Samuel Egwu ya zaiyana zaben a matsayin mafi wuyar sha’ani da ya taba gani tun shigowar sa aikin hukumar zabe a 2017.

Egwu ya ce za ka ga karamar hukuma mai yawan wadanda a ka yi wa rejistar zabe dubu 14 ko dubu 15 amma sai ka ga mutum dubu 1.200 zuwa 1,500 su ka fito don kada kuri’a.

Wannan akasin ba zai rasa nasaba da yanda mutane su ka firgita da barazanar ‘yan tawayen Biyafara ta umurtar mutane su zauna a gida ko su fuskanci mugun hukunci.

Duk da kungiyar awaren ta janye barazanar, amma hakan bai karfafawa akasarin mutane guiwa su fito kada kuri’a ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.