• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

RASHA TA SAMU NASARAR YAKIN MAMAYE UKRAINE

Rasha ta yi kurarin a karshe za ta samu nasarar harin da ta kai na mamaye Ukraine duk da taimakon da yammacin turai ke ba wa gwamnatin Ukraine ta shugaba Vlodymyr Zelenskyy.
Ma’aikatar wajen Rasha ta tabbatar da cewa daukin da yammacin duniya ke ba wa Ukraine na kawo jinkirin yakin, amma dai za ta yi nasarar kwance damarar Ukraine.
Kasar ta Rasha na yunkurin hana Ukraine shiga kungiyar tsaro ta yamma ne wato NATO.
Furucin na Rasha na zuwa ne a lokacin da a ke samun bayanai masu sabawa juna na ceto mutane daga garin Marupol mai tashar jiragen ruwa.
Dubban mutane sun mutu a sanadiyyar wannan yaki kuma garuruwa da yawa sun zama kangaye.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *