• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHA TA KAI HARIN ROKA KAN MASANA’ANTAR KARFE TA MARIOUPOL A UKRAINE

Dakarun sojan Rasha sun kai harin roka kan masana’antar karfe ta Marioupol da ke Ukraine don kara kassara tungar karshe ta gwamnatin Kyiv a yankin.
Marioupol da ke bakin teku na da muhimmanci ga Ukraine wanda hakan ya sa wasu mutane da sojojin Ukraine su ka zauna a ma’sana’antar har sai da majalisar dinkin duniya da kungiyar agajin RED KUROS su ka ceto wasu daga cikin su.
Rasha na kara matsa kaimin hare hare don kwance damarar yakin Ukraine da hana ta samun tallafin makamai daga ketare.
Da alamun Rash a ba ta samun yakin cikin sauki, amma ba ta da muradin kwace kasar Ukraine fiye da burin kwance damarar yakin gwamnatin shugaba Vlodymyr Zelenskyy.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.