Sojojin Rasha sun kai hare-hare kan layukan dogo a daukacin Ukraine don katse wutar lantarki da hana shigo da makamai daga yammacin turai ga gwamnatin shugaba Vlodymyr Zelenskyy.
Hakanan Rasha ta ce ta yi amfani da makamai masu linzami daga sojojin ruwa da na sama don rage karfin sojan Ukraine.
Rasha ta musanta kai hari kan masana’antar karfe ta garin Marioupol da ke zama tashar jiragen ruwa mai muhimmanci a Ukraine.
Kamfanin karfen dai na zama tungar karshe da ke kaekashin gwamnatin Ukraine a garin na Marioupol inda wasu sojojin kasar ke zama don mafaka gabanin samun dauki.
Rasha na daukar matakan gabanin karin hanyoyin karya tattalin arziki da kasashen yamma su ka dauka na hana sayar da man fetur din Rasha.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀