• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHA NA KARA DAUKAR MATAKAN SOJA DON CIMMA BURI KAN UKRAINE

Rasha na daukar karin matakan kwance damarar makaman Ukraine don hana ta tasirin nacewa da shiga kungiyar tsaron yammacin turai NATO.
Ba ma wani abun mamaki a matakan na Rasha don yanda a ke zaman tsama tsakanin ta da yammacin turai tun rushewar tsohuwar daular Sobiyet ta ‘yan gurguzu.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha na da alamun amfani da duk wani karfi don hana karin kasashe a yankin bijirewa hadin kan tsaro na gabashin turai ta hanyar kulla kawancen soji da kasashen yamma.
Yammacin turai musamnan Amurka na bin hanyoyin ladabtar da Rasha bisa wannan mamaya ga Ukraine.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.