• Fri. Sep 30th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RASHA BA TA DAUKAR CEWA TA NA FADA DA NATO AMMA NATO NA GANIN HAKAN-LAVROV

Ministan wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce Rasha ba ta daukar fadan da ta ke yi Ukraine cewa da kungiyar tsaron yammacin turai NATO ta ke yi, amma NATO haka ta dauka.
Lavrov ya shure batun da sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres na bude hanyoyin kai agaji ga fararen hula, ya na mai cewa ‘yan gani-kashenin Ukraine ne su ka hana ba da agajin.
Lavrov ya ce sun godewa matsayar ta Guterres amma ‘yan gani kashenin Ukraine ke biris da kafar isa ga jama’a don taimaka mu su.
Gameda da yiwuwar shiga yakin kasar Maldova, Lavrov ya ce ya kamata Maldova ta damu da makomar ta domin a na neman ingiza ta, ta zama memba a NATO.
Ministan wajen na Rasha ya zargi NATO da jagororin yammacin turai da nuna tamkar yaki su ke yi da Rasha don miyagun kalaman da su ke furtawa na Rasha za ta sha kaye ko dole a kada Putin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.