Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai gadarwa Najeriya tsarin zabe mai inganci inda kuri’ar jama’a za ta rika tasiri.
A jawabin sa mai sakin layi 51 na murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yanci, shugaban ya buga misali da yanda a ka gudanar da zabe a jihar Edo inda jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe zaben.
Shugaban Buhari wanda ya tsaya takara sau 4 a tsawon shekaru 12 kafin lashe zabe a 2015, ya ce in an duba gwagwarmayar da ya yi kan lamuran zabe, ya kai ma’aunin inganta lamuran kuri’a ta rika yin aiki.
Shugaban ya ce kasar Najeriya ba tasa ba ce shi kadai ko ta ‘yan jam’iyyar hamaiya, amma ta dukkan al’ummar Najeriya ne.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Wow, that’s what I was looking for, what a stuff! present here at this blog,
thanks admin of this website.