• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RANAR TUNAWA DA BUDE WUTA KAN YARA BAKAKEN FATA A SOWETO

Majalisar dinkin duniya da kungiyar taraiyar Afurka su ka  ware wannan  rana don tunawa da yaran Soweto na kasar Afurka ta kudu da su ka rasa ransu a shekarar 1976 don suna so su na son damar karatu kamar fararen fata.

Yara kimanin dubu 20 a Soweto 1976 sun gudanar da zanga-zanga don samun damar samun ilimi daidai da fararen fata a zamanin mulkin wariyar launin fata, amma sai jami’an tsaro su ka bude mu su wuta su ka yi kisan gilla ga da yawa daga cikin su.

Shekara talatin kenan da a ka ware 16 ga watan yunin kowace shekara a matsayim ranar tunawa da yaran da suka rasa ransu  a Soweto saboda suna son zuwa makaranta.

Taken ranar na wannan shekarar shine ” shekara 30 bayan cimma yarjejeniya. Zummar aiwatar da muradin shekarata ta 2040 ga kyautata rayuwar yaran Afurka.”  

“El- meela Heritage support foundation” asusu ne mai zaman kan sa da ke taimakon yara  da hadin gwiwar wata kungiyar farar hula mai tallafawa ilimi “civil society Action coalition on education” sun gudanar da taro don jan hankalin masu ruwa da tsaki don ganin an ba wa yara hakkin su musamman ingantaccen ilimi, lafiya, abinci mai gina jiki da sauransu.

A taron a Abuja, shugabar asusun bin kadun yaran “El-meela Heritage support foundation” Barista Jamila Isa Eneka ta ce yanzu kama ko da yara sun samu zuwa makarantar, su na fuskantar barazanar sace su.

Da yake gabatar da jawabi babban sufuritandan civil defence Idoko Samuel ya nuna damuwa da halin rashin tsaro da yara ke fuskanta musamman a makarantu , ya kuma kara da cewa rundunar su ta horos da runduna ta musamman da za ta kula ko tsare yara a makarantu da tabbatar da cewa sun samu cikakken tsaro.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
57 thoughts on “RANAR TUNAWA DA BUDE WUTA KAN YARA BAKAKEN FATA A SOWETO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.