• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RANAR 25 GA FEBRERU 2023 ZA A YI ZABEN SHUGABAN KASA A NAJERIYA

Hukumar zaben Najeriya INEC ta aiyana ranar 25 ga watan Febreru 2022 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa da wakilai.
Shugaban hukumar zaben Mahmud Yakubu ya baiyana sabuwar ranar bayan samun amincewa da sabuwar dokar zabe da shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu.
Farfesa Yakubu ya kuma aiyana ranar 11 ga watan Maris 2022 ta zama ranar da hukumar za ta gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha.
Gaba daya daga yanzu zuwa lokacin babban zaben na 2023 kwana 362 ne.
Masu sha’awar takarar mukamai musamman a manyan jam’iyyu biyu APC da PDP na baiyana muradin su don fara sharer fagen lokacin da za a fara kamfen ko zaben fidda gwani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.