• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RABUWAR KAWUNA A TSAKANIN SHUGABANNIN APC NA TARNAKI GA ZABEN FIDDA GWANI

An samu rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin jam’iyyar APC da hakan ya kawo tarnaki ga zaben fidda gwani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Yayin da shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ke cewa Sanata Ahmad Lawan ne gwanin da a ka canka, sauran shugabannin jam’iyyar na cewa ba da su a ka dau matsayar ba.

Wannan dambarwa ta kai ga gwamnonin arewa na APC su ka gana da shugaba Buhari wanda ya ce sam bai canki wani daga ‘yan takarar ba, don haka a tafi a gudanar da zabe.

Gwamnonin dai da su ka ce sun zabi tikitin jam’iyyar ya koma kudu sun samu mara baya daga akasarin ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

Duk da haka wasu daga ‘yan kwamitin irin su Dattuwa Ali Kumo na cewa ko ma yaya a ka juya maganar gwanin na nan tun ran gini.

Shaharerren dan jam’iyyar Injiniya Magaji Muhammad Yaya ya bukaci jam’iyyar ta gujewa dalilan da su ka sa PDP ta fadi zabe a 2015.

Masanin harkokin siyasa Dr.Abubakar Kari ya ce batun daidatawa ga tsaida dan takara ya kurewa APC.

Za a jira a talatar nan a ga wanda zai zama gwanin na APC wanda zai iya zama wa imma na gwamnoni ko kuma na masu fadi tashin wanzuwa a madafun iko.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.