• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RA’AYOYI NA KARA KARFI KAN KIN JININ 12 GA YUNI A MATSAYIN RANAR DIMOKRADIYYA A NAJERIYA

Yan Najeriya da dama na cigaba da nuna rashin amincewar su da sauya ranar bukin dimokradiyyar Najeriya daga 29 ga mayu zuwa 12 ga yuni.

Gabanin ziwan gwamnatin shugaba Buhari, a kan yi murnar ranar 29 ga wata da ta zama ranar da a ka dawo mulkin farar hula a 1999 bayan dogon mulkin soja.

Shugaba Buhari ya sauya ranar zuwa 12 ga yuni don tuna ranar da a ka soke zaben marigayi Mashood Abiola a 1993 zamanin mulkin tsohon shugaba Janar Babangida.

Madu korafi kan ranar na cewa tamkar raba kan ‘yan Najeriya ne ta hanyar fifita muradun wata kabila kan wata ko yanda sai mutane sun fito zanga-zangar kafin yi mu su abun da su ke so.

Duk da sanya ranar a matsayin ranar dimokradiyya, bai hana yarbawa a kudu maso yamma gangamin tuna ranar ba da hakan kan zama bigiren furta kalamai masu tsauri da barazana ga hadin kan kasa.

Wasu masana na cewa gwamnatin Buhari ta yi siyasa ne wajen karrama ranar don yankin kudu maso yamma da su ka mara baya APC ta lashe zabe su kwantar da hankali kan tunanin dan arewa ya danne hakkin su wajen soke zaben dan uwan su Abiola.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.