• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

POMPEO YA FARA ZIYARA MAI DAWAINIYA TA KASASHE 7 CIKI DA GABAR TA TSAKIYA

Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya fara ziyara mai dawainiya ta rangadin kasashe 7 inda ya fara da kasar Faransa.

Pompeo zai zaga kasashe da su ka hada da yankin gabar ta tsakiya.

Mike Pompeo na wannan ziyara cikin yanayi da za a ce ba bankwana kuma hatta yawancin kasashen da zai ziyarta sun taya Joe Biden murnar lashe zaben shugaban Amurka.

Pompeo da shugaba Donald Trump da sauran manyan ‘yan jam’iyyyae Rifabulikan ba su amince da sakamakon zaben ba.

Pompeo zai ziyarci yankunan matsugunan Yahudawa a yammacin kogin Jodan.

Hakanan zai ziyarci Turkiyya amma ba tare da ganawa da jami’an gwamnatin shugaba Raceb Erdoan ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.