Cibiyar tsaron Amurka Pentagon ta baiyana daukar laifin aikata mummunan kuskure a harin da ta kai da jirgi marar matuki a Kabul babban birnin Adghnaistan da ya yi sanadiyyar kashe mutum 10 ciki da yara 7.
Amurka ta kai harin ne daidai lokacin da ta ke kammala kwashe sojojin ta a karshen watan jiya.
Hafsan sojan Amurka Janar Frank McKenzie ya ce a lokacin harin ya yi amanna cewa mutanen ‘yan DAESH ne da ke barazana ga sojan Amurka don haka a ka harba mu su jirgi marar matuki, amma yanzu an fahimci kuskure a ka tabka don mutanen da yara ba za su zama ‘yan DAESH ba.
Da wannan kenan McKenzie ya ce Pentagon na tunanin biyan diyya ga wadanda su ka rasa ‘yan uwan
su.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Your post are very enlightening and informative. But the only problem I have is it is written in HAUSA. Is there no English version of the news?