• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PDP TA TURA SUNAYEN WADANDA TA KE SON SU MAYE GURBIN GWAMNAN EBONYI DA MATAIMAKIN SA DA KOTU TA SAUKE

Babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP ta tura sunayen wadanda ta ke son hukumar zabe ta yi amfani da su wajen maye gurbin gwamnan Ebonyi Dave Umahi da mataimakin Kelechi Igwe, wadanda babbar kotun taraiya a Abuja ta sauke daga kujera don sauya sheka zuwa APC.
PDP wacce ta ci nasara a karar da ta shigar don sauke gwamnan daga kujera, ta mika sunan Iduma Igariway a matsayin sabon gwamna yayin da Fred Udogu zai zama mataimakin gwamna.
Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya ce hukuncin na alkali Inyang Ekwo zai hana gangancin ‘yan siyasa ta hanyar sauya sheka
Ayu ya bukaci hukumar zabe ta janye shaidar lashe zabe na gwamna Umahi ta mika ga Igariway don yanda Umahi ya yi biris da lemar da PDP ta yi ma sa ya tsaya takara a tikitin ta a 2015 da 2019 amma a ka wayi gari ya sauya sheka zuwa APC.
Hukuncin na Ekwo zai tada balliballin ‘yan siyasa da su ka sauya shekar musamman ‘yan majalisa don hukuncin kazalika ya kori ‘yan majalisar jihar Ebonyi 15 da su ka bi Umahi zuwa APC.
Alkali Ekwo ya ce in an zo zabe jam’iyya a kan zaba ba gwamna ba, don haka duk gwamnan da ya sauya sheka ya sarayar da mukamin sa.
Nan take Umahi ya ce ya na nan daram a kan mukamin sa kuma ya na zargin alkalin da makirci inda ya ce sun rubuta korafi kan sa zuwa hukumar kula da shari’a, hakanan ya ce za su kwabar da hukuncin a kotun daukaka kara.
Umahi ya buga misali da yanda gwamnan Zamfara ya tsallake irin wannan siradin duk da bai yi magana kan bambancin su ba, hukuncin kotu ya ba wa gwamna Matawalle na Zamfara nasara don ba shi ya lashe zabe da tutar PDP ba, amma Umahi kai tsaye da tutar PDP ya hau kujera.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “PDP TA TURA SUNAYEN WADANDA TA KE SON SU MAYE GURBIN GWAMNAN EBONYI DA MATAIMAKIN SA DA KOTU TA SAUKE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.