• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PDP TA TSAWAITA RANAR RUFE SAYAN TAKARDAR NEMAN TAKARAR ZUWA TALATA

Babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP ta tsawaita ranar rufe sayan takardar cikewa don tsayawa takara zuwa talatar nan mai zuwa.
Kakakin jam’iyyar Debo Ologunagba ya baiyana tsawaita wa’adin don cike gurbin hutun mabiya addinin kirista na ISTA.
Jam’iyyar za ta karbi dukkan takardun zuwa ranar larabar nan.
Daga nan jam’iyyar ta sanar da ranakun tantance sunayen dukkan ‘yan takarar don shirin zaben fidda gwani.
Da alamun jam’iyyar ta na da jan aiki ga zaben gwanin dan takarar shugaban kasa don barin kofar takarar a bude ga dukkan sassan kasa.
Gwamnonin jam’iyyar da su ka hada da Aminu Tambuwal na Sokoto da Nyesom Wike na Ribas na son tikitin jam’iyyar, inda tsohon dan takarar jam’iyyar Atiku Abubakar ya sake fitowa da mara bayan jama’ar PDP na arewa maso gabar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “PDP TA TSAWAITA RANAR RUFE SAYAN TAKARDAR NEMAN TAKARAR ZUWA TALATA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.