• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PDP TA MIKA SHIDAR LASHE ZABEN FIDDA GWANI GA ATIKU ABUBAKAR

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta mika shiadar lashe zaben fidda gwani gad an takarar ta ga zaben 2023 Atiku Abubakar.

Shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya mika shaidar a wani kwarya-kwaryar taro a helkwatar jam’iyyar a Abuja.

In za a tuna Atiku ya lashe zaben da kuri’u 371 cikin 767 da a ka kada a zaben da ya gudana a babban filin wasa na kasa da ke Abuja mai lakabin Moshood Abiola.

Gabanin nan Atiku ya zaga don neman goyon baya daga sauran jiga-jigan jam’iyyar har ma da gwamnan Ribas Nyesom Wike wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwanin.

Yanzu za a jira a ga wanda APC mai mulki za ta tsayar ranar litinin mai zuwa.

Wasu jam’iyyu da su ka hada da NNPC da Labor sun tsayar da ‘yan takarar su wato tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.