Babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP a na ta bangaren ta kore labarin da ‘yan APC su ka dauka cewa a Lagos za ta yi zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa, ta na mai cewa za ta yi taron a rufeffen dandalin wasa na filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja ranar asabar 28 ga watan nan na mayu.
A bisa yanda APC ke sauya ranakun taro, PDP ta bakin mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa Ambasada Umar Iliya Damagun ya ce APC na koyon logar siyasa ne.
Da alamun kowacce daga manyan jam’iyyun za ta so tsayar da wanda ya fi na ‘yar uwar ta tasiri a kudu da arewa.
Bayan kammala jera sunayen ‘yan takara, jam’iyyu za su mika sunaye ga hukumar zabe zuwa uku ga watan mayu.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀